Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Alexis Sanchez
Alexis Sanchez

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, mai horar da ‘yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya nuna sha'awarsa wajan sayen dan wasan gaba na Arsenal Alexis Sanchez.
Guardiola ya ce har sun fara tattaunawa da dan wasan ta wayar salula a bayan wasan da Arsenal tayi da West Ham, a gasar firimiya makon da ya gabata inda Sanchez, ya zurara kwallaye har ukku a ragar West Ham.

Shi kuwa Adam Lallana, na Liverpool ya ce bai da niyyar barin Kungiyar a yanzu, koda yake kungiyar PSG ta nuna sha’awar zawarcin dan wasan.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na zawarcin dan wasan gaba na AC Milan, mai suna Carlos Bacca, mai shekara talatin da haihuwa akan kudi fam miliyan £20.

A tarayyar Najeriya, kuwa bangaren firimiya na kasar Bature Yaro na Nasarawa united, da Richard Jonathan na FC Hearts sun rattaba hannu a Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist, dake garin Bauchi.

A can Gombe, kuwa Gombe united, ta karbi bakuncin ‘yan wasa biyar daga Kungiyar Kano Pillars, wadanda suka zo domin fara takawa kungiyar ta Gombe united, leda, ‘yan wasan sune Adamu Hassan, Munir Ubale Umar Zango Sauran sun hada da Usman Mohammed da Aka kalalaka Wanda dama tsohon dan wasan Gombe united ne a shekarun baya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:37 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG