Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Brazil US Soccer
Brazil US Soccer

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, Kungiyar kwallon kafa ta Manchester united, ta sake nuna sha'awarta wajan zawarcin dan wasan kasar Brazil Mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona mai suna Neymar, Manchester ta kuma warewa dan wasan zunzurutun kudi har fam miliyan £180,

Ozil da De Maria, na sha'awar komawa tsohowar kungiyarsu ta Real Madrid, Juventus da Inter Milan na neman Matteo Darmian, daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.

Everton na shirye shiryen sayan dan wasan Tottenham mai suna Mousa Sissoko, a watan Janairu na dubu biyu da sha bakwai da zaran anbude hada hadar ‘yan wasa kwallon kafa.

Ita kuwa Leicester City, na zawarcin dan wasan tsakiya na Sporting CP Mai suna Adrien.

Kungiyoyin kwallon kafa da dama ne ke zawarcin Shahararren dan wasan kwallon kafan nan Lionel Messi, Wanda suka hada da Irin su Manchester united PSG da Manchester City da dai sauransu a yanzu haka Kungiyar Inter Milan ta shiga sahun neman dan wasan domin ganin ta kawo shi kungiyarta a tsakiyar kakar wasan kwallon Bana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:18 0:00

XS
SM
MD
LG