Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Lionel Messi
Lionel Messi

A hada hadar zaratan ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, na zawarcin dan wasan tsakiya kuma kaftin a Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles na Najeriya mai taka leda a Kungiyar Chelsea mai suna Mikel Obi.

Juventus ta na neman Yaya Toure daga Kungiyar Manchester City a watan janairu mai zuwa idan aka bude sayen ‘yan wasan kwallon kafa na shekarar da zamu shiga.

PSG ta fara tattaunawa da ma'haifin Shahararren dan wasan kwallon kafar kasar Argentina, mai taka leda a Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, mai suna Lionel Messi, domin ya takawa kungiyar ta PSG leda.

AC Milan tana bukatar Isco na Real Madrid da ya komo Kungiyar a tsakiyan kakan wasan bana, inda kuma, Fenerbahce na shiri domin sayan dan wasan gefe na Manchester City mai suna Jesus Navas.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG