Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A Hada Hadar yan wasan kwallon kafa na duniya, mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho, ya musanta rade radin da akeyi cewar yana zawarcin Shahararren dan wasan kwallon kafa na Barcelona mai suna Lionel Messi.
Mourinho, ya kara da cewa yana da yakinin dan wasan zai gama taka ledarsa ne a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
Har ila yau kungiyar ta Manchester United, tana yunkurin karawa dan wasanta mai suna Zlatan Ibrahimovic, tsawon kwantareginsa a kungiyar inda take sa ran dan wasan zai kai shekara ta 2018 a kungiyar ta Manchester United.

Shi kuwa dan wasan tsakiya na Real Madrid, Isco ya nuna jindadinsa ne da zamarsa a Kungiyar inda yake sha'awar tsawaita kwantareginsa nan gaba a kungiyar ta Real Madrid. Inda kungiyar, Wolfsburg tace dan wasanta mai suna Julian ba na sayarwa bane.

Shima dan wasan baya na Arsenal Laurent Koscielny dan shekara talatin da daya da haihuwa yace tsakaninsa da Kungiyarsa ta Arsenal mutu ka raba domin anan ya keso ya kare kwallonsa har lokacin da zai ajiye takalmansa na taka leda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:12 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG