Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zarantan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


 Steven Gerrard
Steven Gerrard

A hada hadar ‘yan wasan kwallo kafa Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, na zawarcin dan wasan Juventus mai suna Alex Sandro.
Yayinda Everton na neman dan wasa daga Kungiyar Chariton mai suna Ademola Lookman, Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, na tsawaita kwantaregin dan wasanta maisuna Chris Smalling ne.
Kungiyar kwallon kafa ta MK Dons ta yiwa tsohon dan wasan kasar Ingila wanda ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Steven Gerrard, tayi na zama mai horar da ‘yan wasa a kungiyar.
Sai dai har yanzu Gerrard mai shekaru talatin da shida da haihuwa baice komai bisa tayin da aka yi masa,
koda yake a kwanakin baya tsohuwar Kungiyarsa ta Liverpool, tayi masa irin wanan tayin.
Daga karshe Manchester United na yunkurin sayen dan wasan baya na Bayern Munich mai suna David Alaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:10 0:00

XS
SM
MD
LG