Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Luis Suarez
Luis Suarez

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, na zawarcin dan wasan Barcelona mai suna Luis Suarez.

Tottenham na neman Isco daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, CSKA Moscow na kasar Rasha na neman dan wasan gaba na Wikki tourist dake Bauchi a Najeriya, mai suna Godwin Obaje, dan wasan da yafi kowa jefa kwallo a gasar firimiya lig na Najeriya, a bana.

Shi dai Godwin Obaje, ya zurara kwallaye har guda goma sha takwas a raga a cikin wasannin 36 da aka fafata a gasar ta firimiya a bana.

AC Milan na shirin sayen dan wasan Manchester United Bastian Schwenteiger.

XS
SM
MD
LG