Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, dake Ingila na zawarcin dan wasan baya na Barcelona mai suna Yerry Mina, mai shekara ashirin da biyu da haihuwa.

Itama Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan na neman dan wasa mai suna Marco Verratti, wanda kungiyoyin Arsenal da Chelsea suma ba’a barsu a bay aba wajan zawarcin sa.

Arsenal da Manchester United, na zawarcin dan wasan PSG mai suna Edinson Cavani.

Real Madrid da kungiyar kwallon kafa ta PSG na neman dan wasan Liverpool mai suna Philippe Coutinho, sai dai shi wannan dan wasan ya fi sha'awar zuwa Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00

XS
SM
MD
LG