Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jose Mourinho Ya Ce Wayne Rooney Ya Nemi Kulob


A hada hadar 'yan wasan kwallon kafa na duniya, kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan na kasar Italiya na zawarcin dan wasan kasar Ingila kuma kaftin a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United mai suna Wayne Rooney dan shekara 31 da haihuwa.

Rooney wanda ya bugawa Manchester United, wasanni goma sha biyu a bana ya jefawa kungiyar kwallo daya tilo ne a raga a bana, inda a kwananna ne Mai horar da kungiyar Jose Mourinho ya umurci Rooney da ya neme wata kulob matukar yana so ya ci gaba da wasan kwallon kafa amma ba a Manchester United ba

PSG na neman dan wasan gaba na Atletico Madrid, mai suna Antoine Griezmann, ita kuwa Liverpool ta fara zawarcin dan wasan tsakiya na Dinamo Zagreb, mai suna Ante Coric dan shekara sha tara da haihuwa shi dai wannan dan wasa Kungiyar Real Madrid da Barcelona na zawarcinsa.

Manchester United na shiri domin sayen dan wasan baya na gefen dama Nelson Semedo daga Kungiyar Benfica akan kudi yuro miliyan €40, Arsenal na neman dan wasa daga Kungiyar Middlesbrough mai suna Harry Chapman.

XS
SM
MD
LG