Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar 'Yan Wasan Kwallon Kafa Ta Duniya


Kungiyar Real Madrid za ta fuskanci takara daga Manchaster United da Bayer Munich don dakko dan wasan gaba na kulab din Liverpool, Mohamed Salah, a wannan kakar wasannin, a cewar rahotonni daga Spain.

Wasu kulab biyu da suke kasar China, Guangzhou Evergrande da Shanghai SIPG. Suna neman dan wasan gaba na kulab din Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, wanda aka yi masa tayin kusan fan miliyan dubu 300,000 a duk sati.

Juventus Tana so ta sake dakko dan wasan tsakiya na kulab din Machester United da Faransa, Paul Pogba a wannan kakar wasanni mai zuwa.

Dan wasan gaba na kulab din Liverpool, Divock Origi ya sake samun sabuwar kwantiragi a Anfield, bayan da ya ci kwallaye a manyan wasanni na wannan kakar wasan a bana - ciki har da wasan karate na cin kofin zakarun turai na Champion League.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG