Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwagwarmaya A Kasar Saudiya


Takaran Kasar Saudiya

Wani mazaunin kasar Saudiya mai suna Ibrahim Khalil wanda ya shafe shekaru fiye da 20 yana zama a can, ya bayyana cewa yanzu babban tashin hankalin da suke fuskanta shine ana kama wadanda da basu da takardar zama a kasar .

Malam Ibrahim Khalil ya kuma ce nema ne ya ka kai shi Saudiyya bayan ya kammala karatunsa na sakandare.

Aikin wankin mota a jami’ar Makkah Malam Ibrahim ya fara bayan isar sa kasar, daga nan kuma ya fara sana’ar hannu, bayan haka ya sami aiki a wani kamfani mai suna Bil-ladan .

A shekarun da suka gabata gwamnatin kasar Saudiya ba ta takurawa wadanda suka zo ci rani daga wata kasa ba kamar yadda ake takurawa marasa takardar zama kasar yanzu ba, ana kuma kama wadanda basu da takardar Igama.

Ibrahim Khalil ya kara da cewa rayuwa a Saudiya ba ta da dadi a yanzu, domin ko masu takardar zama kasa ana takura musu.

Saurarin cikakken rohoton mu daga Baraka Bashir

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:12 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG