Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwaggo Calaya Ta Haihu A Gidan Zoo


Da misalin karfe daya na dare ne a ranar lahadin da ta gabata Becky Melinsky wacce ke aiki a Gidan ajiye namun daji na kasa bangaren birai taje duba bangaren da Calaya Gwaggon biri mai dauke da tsohon ciki.

Melinsky dake taimakawa wajen kula da wadan nan namun daji ta ga alamun Calaya bata jin dadi jim kadan da ta kara dubawa sai taga ashe Calaya nakuda take, Melinsky bata yi kasa a gwiwa ba take ta kira wayar mai kula da gidan namun dajin ta bashi labari.

A sa'o'i biyar Calaya ta kwashe tana nakuda inda daga bisani ta haifi zan kadeden jaririn biri, daga gefe guda ma’aikatan da ke kula da namun daji kuwa suna daukar hoto yadda lamarin ya kasance.

Ma’aikatan kula da namun dajin sun ce nan take sauran birai da ke cikin wannan gida suka fara tsalle da ihu da ke nuna farin cikin su, Baban namijin Gwaggon birin kuwa wanda ake kira Baraka, mai nauyin Fan 450 yayi ta muzurai yana nishi alamun da ke nuna farin cikin sa da samun magaji.

An radawa jaririn birin suna Moke, wanda ke nufin karami a yaren Lingala na Afirka ta tsakiya ko kuma muce a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo inda wadannan birai suka samo asali. Mai jego da Jaririnta suna cikin koshin lafiya. Babban dalilin da yasa wannan labari ya zama labari shine, Jinsin Gwaggon birin dai na fuskantar barazanar karewa.

Mun tsakuro wannan labari ne daga Jaridar Washington Post Nazir Ahmed Hausawa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG