Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Goyon Bayan Magidanta Na Taimakawa Wajen Samun Daukaka


Malama Halima Waziri

Halima Waziri mai aikin jinya, ta ce tun da ta fara karatunta da son zama jami’ar jinya, harkokin ta na tafiya da kyau, da samun nasara don Allah ya bata sa’a ta samu gurbin karatu a fannin lafiya, bayan kammala karatun ta, kuma ta samu aiki a matsayin 'Community Health Extension Worker.' Malama Halima ta ce ta fara aiki a karamar hukumar Tarauni, a matsayin ma’aikaciyar lafiya a mataki na farko, bayan nan ta samu canjin ayyuka a wasu kananan hukumomin da suka hada da karamar hukumar Birni da sauransu.

Ta kara da cewa a yanzu haka ta samu cigaban da yanzu take asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda take aiki a matsayin Chief Community Health, inda a yanzu take da ma’aikata a karkashinta.

Ta bayyana cewa kafin ta kawo ga wannan matsayi sai da ta karo karatu, kuma ta ce tun da ta fara aiki kimanin shekaru goma da suka wuce, bata taba samun wata matsala ba da abokan aiki ko wasu da take hurda da su ba.

Mun tambaye ta ko yaya take hada aure da aiki? sai ta ce mai gidan ta ya bata goyon baya, da taimaka mata wajen jajircewa da mai da hankali da samun daukakar da ta kai a yanzu.

Saurari cikakken rahoton wakilyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG