Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Golden Eaglets Na Shirin Tunkarar Gasar 'Yan Kasa Da 17 a Brazil


'Yan wasan Najeriya suna atisaye

Za a fara gasar a ranar 26 ga watan Oktoban bana inda Brazil za ta karbi bakuncin gasar.

Dan wasan gaba na kungiyar kafa ta Nasarawa United, Sunusi Ibrahim, na daya daga cikin ‘yan wasa 52 da Golden Eaglets ta gayyata zuwa sansanin atisaye, a wani mataki na shirin tunkarar gasar FIFA ta cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17, wacce za a yi a Brazil.

Za a fara gasar a ranar 26 ga watan Oktoban bana inda Brazil za ta karbi bakuncin gasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Najeriya ta samu gurbin shag gasar ce, baayn da ta kare a cikin kasashen hudu da suka yi zarra a gasar cin kofin zakarun Afirka ta ‘yan kasa da shekaru 17, wacce aka yi a Tanzania a watan Afrilun da ya gabata.

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar ta Najeriya, Manu Garba, ya nemi ‘yan wasan da suk hallara a otel din Serob Legacy da ke Abuja.

Najeriya ta lashe kofin gasar a shekarun 1985, 1993, 2007, 2013 da kuma 2015.


  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG