Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Cinyesu Duk


Wata gobara da ta tashi a tsakar dare ta yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu ‘yan gida daya wanda aka sani da iyalin Eze wadanda suke gida mai lamba 13, akan titin Buraimoh dake unguwar Bariga a jihar Legas.

Daraktan kungiyar ‘yan kwana kwana na jihar Legas Mr. Rasak Fadipe ne ya tabbatar da aukuwar al’amarin ga manema labarai a Legas cibiyar kasuwancin Najeriya a yau laraba inda yace abin ya faru ne kimanin karfe 2 da minti 48 na dare.

Ya ce ma’aikatan kwana kwana sun isa wurin jim kadan da suka sami labari amma kash, basu samu damar ceton mutanen ba saboda makarin karfen dake jikin tagogin gidan.

“ Gidan nasu wani shagon saida magunguna ne, inda iyayen da yaransu biyu masu shekaru 5 da 8 sun mutu a ciki”.

Daraktan ya bada shawarar cewa mutanen na bukatar tsaro a gidajen su, bai kamata kuma ace neman hakan yasa sunyi abinda zai taba lafiyarsu ba, mutanan gida dole su san hanyar fita daga gidajen su idan irn haka ta faru”.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa matar data rasu tana dauke da juna biyu kuma wutar ta tashi ne bayan da aka maido da wutar lantarki wasu kuma sunce wata kila kyandir ne yayi sandiyyar gobarar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG