Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Na Tashe A Fasahar Kirkire-Kirkire


Fathia Ayodele Kareem, wata 'yar Najeriya da ta lashe kusan dukkannin lambobin yabo a jami'ar koyon aikin likita na birnin Akkra (Accra) na kasar Ghana.
Fathia Ayodele Kareem, wata 'yar Najeriya da ta lashe kusan dukkannin lambobin yabo a jami'ar koyon aikin likita na birnin Akkra (Accra) na kasar Ghana.

Ana daukar Ghana a matsayin wani babban fagen inganta fasahar kirkire-kirkire a Yammacin Afurka, ganin yadda matasan kasar ke dada bullo da hanyoyin amfani da dabarunsu na kashin kansu wajen warware matsalolin kasar. Hasali ma a watan Disamba mai zuwa kasar za ta karbi bakuncin wasu manyan taruka kan dabarun kirkire-kirkire da fasaha.

A wannan rahoton da Stacey Knott ta hada ma na, daya daga cikin wadanda su ka kirkiro fasahar Recycle Up!, mai suna Alhassan Baba Muniru na da burin tsaftacce muhalli a Ghana.

Bugu da kari, Alhassan na so ya ilimantar da matasan Ghana, ya tayar masu da komada ya kuma karfafa masu gwiwa – duk saboda su rumgumi al’adar kare muhalli, amma kuma ta yadda hakan zai janyo masu kudi, wato riba biyu.

A babban taron fasahar kirkire-kirkiren Afurka da za a yi a birnin Akkra (Accra) na kasar Ghana, Alhassan na shirin yin kiran da a dada bayar da himma wajen tallafa ma matasa masu fasahohin kirkire-kirkire, musamman ma masu niyyar bunkasa nau’ukan fasahohi masu kare muhalli.

Alhassan ya ce, “Duk da yake a yanzu mu dalibai ne, tuni mu ka zama ma’abuta sana’o’i. Na san zan iya aiki a wata ma’aikata, amma saboda ‘yancin da ke tattare kirkirar abin da basirarka ta nuna ma ka da kuma jagorantar wata harka a aikace kuma wadda za ta inganta al’umma, abu ne da ya fi gamsarwa.”

Stacey ta cigaba da matakan da Recycle Up yake daukawa sun hada da kwashe tarkacen leda da roba daga makarantu don sayar ma mutane irinsu Nelson Boateng, wanda kamfaninsa ke garwaya su da yashi ya kirkiro bulo (tubula).

Muniru da Boateng sun yi tattaki cikin kamfanin wanda ke wajen birnin Akkra (Accra), inda ake nika tarkacen leda da roba din a kuma narkar da su, a cakuda su da yashi sannan a mai da su bulo, wadanda ake amfani da su wajen gina hanyoyi da lawali da kuma gine-gine.

Boateng, wanda ke kuma yin jakunkunan ledoji, ya ce yin bulo din wata hanya ce da ya ke taimakawa wajen tsaftacce muhalli da kuma samar da ayyukan yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG