Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gerard Pique Ya Ce Zai Yi Kyau Paul Pogba Ya Koma Nou Camp


Paul Pogba

Dan wasan baya na Barcelona mai suna Gerard Pique, mai shekaru 31, ya ce "zai yi kyau idan dan wasan Manchester United, Paul Pogba, mai shekaru 25, ya koma Nou Camp a nan gaba.

Dan wasan Chelsea da Ingila Gary Cahill, mai shekaru 32, ya ƙuduri aniyar cigaba da zama a kulob dinsa na Chelsea duk da yake fama da rashin shiga tawagar Kocin kungiyar Maurizio Sarri.

Tsohon dan wasan Arsenal d Thierry Henry, mai shekaru 41, na duba yuwuwar zama a kungiyar Bordeaux a matsayin kocinta saboda tsoron rashin kudi a kulob din.

Matashin dan wasan baya na West Ham, mai suna Reece Oxford, mai shekaru 19, yana shirin komawa kungiyar Eibar na kasar Spain a matsayin aro inda suke son biyan kudi fan miliyan 1.8.

Dan wasan Roma da Netherlands Kevin Strootman, mai shekaru 28, ya yanke shawarar kammala shekaru biyar a Serie A ta hanyar komawa Faransa don shiga Marseille kan kudi fan miliyan £ 22.6m.

Tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea kuma dan wasan Brazil Ramires, mai shekaru 31, yana kusa da sake shiga Benfica a kan aro daga Jiangsu Suning ta kasar Sin.

Paris St-Germain sun yi watsi da "hasashe da ake danganta su da dan wasan Tottenham da Denmark dan wasan tsakiya mai suna Christian Eriksen, mai shekaru 26, a duniya.

Manchester United, sunki amincewa game da zawarcin da kungiyar AC Milan da kuma Atletico Madrid suke yi domin sayen Martiard Anthony mai shekaru 22 da haihuwa. Dan wasan mai tsaron gida na Belguim da Liverpool Simon Mignolet ba zai bar Liverpool kafin karshen saye da sayarwa na kakar wasa ta Turai ta ban aba, dan wasan mai shekaru 30 na da damar samun kansa a cikin ‘yan wasan farko a kungiyar.

Arsenal na kan gaba wajan kulla yarjejeniya tare da kamfanin Adidas, na tallafin kudi fam miliyan £300m kasancewar kwangilarta da Puma da ta kare a karshen kakar wasa ta bana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG