Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fim Din Race 3 Ya Yi Gagarumar Riba Cikin Kwanaki Uku


Bai zama da mamaki ba cewa fim din Race na uku ya samu kudi fiye da RS 100 a cikin kwanaki uku kacal, kuma da alamun cewa ya haura da RS 10 tun Juma’ar makon Jiya zuwa Asabar, lamarin da y aba jama’a da dama mamaki, hakan zai iya faruwa da fim din Salman Khan ne kadai.

Samun ribar RS 106 da digo 47 a cikin kwanaki uku kawai ya sa fim din Race na uku ya zama fim mafi sauri wajen samun irin wannan kudin.

Salman Khan ya sha tabbar da cewa fina finan sa sun samu kudin da ya kai kimanin RS 100 cikin kwanaki uku da sakar sa a cikin fina finan sa wanda ya fi samun nasara dai shine fim din SULTAN wanda ya samu kudin da ya kai RS 180. Duk da cewa kwanaki 5 kawai aka baiwa fim din ya nuna a gidajen kallo.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG