Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fim Din Akshay Kumar LLB 2 Na Cin Kasuwarsa A Bollywood


India Bollywoods Big Earners
India Bollywoods Big Earners

Daga dukan alamu fim din Akshay Kumar, mai suna LLB 2, yana cin kasuwarsa a Bollywood, wannan fim din da ya fito ranar 10, ga wannan watan da muke ciki ne ya kuma samarda tsabar kudi fiye da dalar Amurka miliyan goma sha daya da dubu dari biyar a cikin kwanaki biyar kachal.$11,500,000.

Fim din da a yanzu haka ke makon sa na farko, a Bollywood, ya kasance ci gaban fim din Akshay Kumar, na Courtroom drama ne wanda ya shirya a shekarar 2013.

A wancan lokacin jarumai kamar su Arshad Warsi da Boman Irani, ne suka fito a Courtroom drama.

Dubin Jama’a a Bollywood, sun karbi fim din LLB 2, da hannu biyu biyu, har masu kushe suma sunyi na’am da fim din domin an nuna bajinta da kimiyar zamani a ciki.

Hata abokan gogayyarsa a Bollywood, kamar Hrithik Roshan da Arshad, suma sun jinjina masa akan wannan nasarar da ya samu a shirya fim din.

Ana kuma sa ran cewa fin din na iya samun miliyan 16, a ciki mako daya ganin yadda fim din ke cin kasuwarsa a Bollywood, kuma a yanzu haka babu wani fim da zai taka masa birki.

Koda yake sai da aka kai masu gabatar da fim din kara kotun ranar 6, ga wata kwanaki 4, kafin fitowar fim din, inda wasu lauyoyi ke kalubalantar cewa akwai wuraren da yake nuna su a matsayin na ba daidai ba inda alkali ya umarci a yanke wuraren kuma aka aiwatar da umarnin kotu a cikin kwanaki uku kafin fitowar fim din ranar 10, ga wata.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:30 0:00

XS
SM
MD
LG