Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farin Jinin Rajinikanth Ga Masoyan Sa A Fadin Duniya Tamkar Al'ada


Jama'a da dama sun bayyana cewa Rajinikanth yana da mabiya da yawa ta yanar gizo a fadin duniya kuma mafi yawancin masoyansa tamkar suna fita haiyyacin su da zarar sun ji labarin sa.

Yayinda da aka saki sabon fim dinsa, mun san cewa mabiyansa za su jeru a layi a wajen gidajen kallon fina finai, ko silma, tun daga karfe 4 na safe domin kallon fim din sa.

Babban abin mamaki anan shine yadda masoyansa mata da maza da suke shiga jirgi daga wasu kasashe kawai dan zuwa kallon film din sa, misali kwai wasu ma'aurata biyu daga kasar Japan da suke zuwa Chennai domin kallon fim dinsa a kowace shekara.

Yasoda da matar sa, su kan shiga jirgin sama tun daga kasar japan zuwa Chennai, domin tabbatar da cewa sun samu ganin fim da aka shirya fitarwa karo na farko da karfe 4 na safiyar da aka fitar da shi, musamman wanda za a nuna a gidan kallon fin na Rohini dake Chennai, a kasar Indiya.

Fim din sa mai suna KAALA tees da fuskar Rajinikanth a ciki, ya sa wadannan Ma’auratan sun yi murna kwarai da gaske domin kallon fim din, amma ga dukkan alamu jama'a da dama sun gane cewa wannan ba shine zuwan ma'auratan India karo na farko domin Kallon fim din Rajinikanth ba.

Yayin da aka tattauna da su a gidan talabishan din NDTV, ma’auratan sunyi bayanin cewa, al’ada ce gare su zuwa Chennai a duk lokacin da aka saki fim din Rajinikanth, saboda fim din baya fitowa a Kasar su Japan, sai daga baya kuma basa son a bar su a baya ko a basu labari.

A cewar Rohoton Bollywoodlife, Mabiyan Rajinikanth, da masoyansa a fadin duniya, koda daga Indiya ne, Faransa, ko Singapore, a nan dai ana ta bikin fitar sabon fim din sa cikin yanayi dabam dabam, wasu ma har bauta masa suke yi suna rawa suna waka.

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG