Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Zata Cigaba da kai Hare-Hare kan Mayakan ISIL a Iraqi


Jirgin Faransa
Jirgin Faransa

‘Yan majalisar Tarayya a Faransa sun amince akan cigaba da kai hare-haren sama akan mayakan ISIL a Iraqi, misalin mako daya kennan bayan harin da wasu maza guda uku, wadanda suka ce suna da alaqa da kungiyoyi masu tsatsaurar ra’ayi a birnin Paris, suka kashe mutane goma sha bakwai.

Da yake magana a gaban majalisar kafin jefa kuri’a jiya Talata, Firayim Ministan Faransa Manuel Valls yace kasarsa na yakar masu tsautsaurar ra’ayi ne, ba addini ba.

Shugaban Hukumar ‘Yan Sandan Tarayyar Turai, da aka fi sani da Europol a jiyan dai ya bayyana cewa misalin mutane dubu biyar ne daga Tarayyar Turai suka shiga yakin Siriya, lamarin dake jawo zaman dar-dar saboda gudun kar wasu daga cikinsu su dawo gida, suna kai hare-hare.

Kasar Faransa na daya daga cikin kasashen Tarayyar Turai da yankin Gabas ta Tsakiya wadanda suka hada gwiwa da Amurka domin yakar mayakan ISIL dake kame da ikon manyan yankuna a Syria da Iraqi a tun shekarar data wuce.

XS
SM
MD
LG