Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadawa Juna Gaskiya ne Zai Kawo Zaman Lafiya


Jihar Taraba
Jihar Taraba

Tun farkon wannan shekaran kawo yanzu rayuka da dama suka salwanta, sakamakon fadace-fadace, a wasu sassan kudancin jihar Taraba, rikicin da kan rikida ya koma na kabilanci ko na addini.

Mukaddashin Gwamnan jihar, Sani Abubakar Danladi, a wani mataki na kawo karshen rikice-rikicen yasa shi ganawa da Sarakunan jihar.

A ganawarsu mukaddashin Gwamnan yayi barazanar daukar mataki da ya dace ga duk wadda ke da hannu a rikice-rikicen dake faruwa a jihar.

Ya kuma ce “ idan muka ce zamu dogara kawai ga ‘yan Sanda ko Sojoji biyan bukata ba zai samu ba, mu sauwakama kanmu, da Gwamnati, mu fadawa junamu gaskiya, ta wajen fadi gaskiya ne zamu samu saman lafiya, mutanen da aka sani cewa mugaye ne, Sarakuna su fidda su a mikawa jami’an tsaro.”

A saurari sauti domin jin karin bayani.

Ganawa da Sarakuna 3'12"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG