Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Kabilanci ya Sake Kunno Kai a Jihar Filato


Wani rikici ya barke a wasu kyauyen kantoma dama wasu kyauyuka, a karamar hukumar Mangu, a jihar Filato, inda aka samu hasaran rayuka da dukiya, da kawo yanzu ba’a tantance ba.

A cewar kansila mai wakiltan Mangu Halle, Yale Abednego, rikicin an fara shine tun ranar Lahadi, bayan da aka yiwa wani mutun kisan gilla, wanda kuma ya kasance wakili ne a zaben fidda gwani na PDP da aka gudanar.

Daga dukkan alamu dai rikicin na kabilanci ne tsakanin Fulani da kabilun yakin na Mangu, wanda yayi sanadiyar rasa rayuka da dama.

Kabilun na yankin na zargin Fulani da kisar gilla, suma Fulani na zargin kabilun da kisa da kuma satar Shanu.

Bayanai na nuni da cewa jami’an tsaro sun kai dauki domin kwantar da rikicin, alumar yankin mahadar Yelwan Shandam da Lantang ta kudu sun bukaci da a girke masu jami’an tsaro saboda kwanton baunar da ake yi ana kashe mutane a hanya.

Rikicin Kabilanci - 3'42"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

XS
SM
MD
LG