Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadakar da Matasa Akan Dabi’u da Basu Dace ba


Matasa a fusace
Matasa a fusace

A shirin mu na nishadi a yau mun sami bakwancin mawaki Sharif Umar Ambulu- wanda akafi sani da Umar Ambulu , ya ce ya fara harakar waka ne kimanin shekaru 13 da suka wuce sanadiyar dan uwansa Sadi Shidi Sharifai.

Ya ce yana samu basirar waka ne a yayin da yake nishadi ko cikin yanayi na abin tausayi , ko da ya ke dan uwansa Sadi Sidi ya taimaka masa ainun domin ya hada shi da wasu fitattun mawaka wadanda suka taimaka wajen gogar da shi a harkar waka.

Ambulu dai ya ce ba abinda ya ke bashi farin cikin illar fadakar da matasa dangane da wasu dabi’u da basu dace da tarbiyar alummar da suke cikin ta ba.

Ya ce fatan sa ya bar baya ko da bayan ransa a tuna shi a ce lailai ya bar wani abu mai muhimmanci a cikin alummar sa.

Ga al’adar wannan shirin kamar kullum Dandali ya yi wa mawaki Umar Ambulu titsiyen aiti daya ga dandali

A fannin shegumi kuwa a kokarin da masa’anatar fim ke yi na farfado da shirya fina-finai wasu manya daga cikin masu ba da umarni da shirya fina-finai za su fara tafiya Ingila don samu horo.

XS
SM
MD
LG