Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Abunda Kake Gudu Sai ya Faru Mutuwace Kowa Sai ya Mutu


Najeriya Zaben 2015 Buhari Jonathan
Najeriya Zaben 2015 Buhari Jonathan

Bayan ga rikicin tsagerun Niger Delta, da fadar kabilanci ko addini a tsakiyar Najeriya, rikicin Boko Haram, tun 2009, ya kai mizanin durkusar da Najeriya.

Shugaban rundunar adalci, Abdulkarim Dayyabu, ne yayi wannan harsashen a hirar su da wakilin muryar Amurka Nasiru Adamu El- Hikaya, yace ya dace masu neman takarar siyasa a dukkan matakai, su fadi dabarun magance kalubalen tsaro har dai zasu samu kuri’un jama’a.

Yana mai cewa “Maganace sai an zo anyi garambawul, a kwatowa kowa hakkinsa an dankamasa a hannu, wanda aka kashe masa Uba, a biyar shi diyyar Ubansa, wadda aka kashe masa Dan a biyashi diyyar Dan sa, wanda aka kashe masa mata ko kani ko wani dan uwa a biyasu diyyarsu, amma matukar ba haka akayi ba yaudaran kanmu zamuyi duk abunda kake gudu sai ya faru mutuwace kowa sai ya mutu sai dai in lokaci baiyi ba saboda haka maganace na yaudaran kai mutane suna ganin cewa kada ayi kasa kada ayi kasa,toh duk kar ayi kasa din, kakanin mu da Iyayen mu duk da suka mutu su dama don suna so su mutu ne, kai in baka so ba zaka mutu ba, ba’a ce ka kashe wani ba don ka rayu, kuma ba’a ce wani ya kashe kaba don ya yaru, kada mu yarda da irin wannan abun ya dore.”

Mayan jam’iyu biyu na Najeriya, na nuna basu alaka da duk wata fitina, inda a yawanci lokuta su kan zargi juna da karya kudurin yarjejeniyar, salama ta kamfe.

Matasan jam’iyyar adawa dai na shirya wani gangamin tabbatar da an gudanar da zabe a watan gobe lafiya, inda kuma wasu lauyoyi suka shigar da kara na neman dakatar da zaben da koma haramtawa dan takarar adawa tsayawa kan takardamar takardar gama sakadare.

Diyyar wadanda aka kashe - 2'49"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG