Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Abin Da 'Ya Mace Ta Fita Nema Shi Za Ta Tarar


Zuwaira Jibrin Gidan Maza, wata uwa ce mai ‘ya ‘ya 5 wacce ta ce ta fara sana’a ne sakamakon mutuwar mijinta gudun kada ta tsunduma ga harkar bara akan tituna.

Malama Zuwaira, ta ce ta fara sana’a ne da sana’ar dinke-dinken zannuwan gado, jaka da sauran kaya da suka danganci mata, koda shike bashi ya karya mata jari har ta hakura ta fara aiki a wani gidan saida abinci.

Malama Zuwaira ta kara da cewa bayan ta fara aikin ne a wani gidan abinci inda ake biyan ta kullum bayan ta kammala aikin ta na wannan rana, da hakan ne ta kula da ‘ya ‘yan ta har ta samu damar lura da makarantunsu da ma kashe wa kanta kananan bukatu.

Zuwaira ta ce abinda ke ci mata tuwo a kwarya baya wuce yadda take ganin wasu mata ke yawon bara da sunan suna neman abinda zasu kula da ‘ya ‘yansu ba, a cewarta duk abinda mace ta fito nema shi zata tarar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:01 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG