Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubun Wani Matashi Ta Cika


Masu gadin kasuwar Igbudu dake Warri a jihar Edo, sun kama wani yaro dan shekara 18 mai suna Avwerouso Esekomeh da laifin yiwa wani Fasto fashi tare da sace mishi wayar salula a kasuwar ta Warri a ranar Litinin 3, ga watan Disamba da kimanin karfe 8 na dare.

Rahotanni sun bayyana cewa barawon ya hadu da sauran mutane a titin Old Welfare lokacin da ake neman wayar da ya sace amman Faston yai maza ya dawo kana yaja hankalin jama’a a lokacin da yaga wanda ake zargi a cikin masu neman wayar.

Victor Igbu wanda yake yawan wa’azi a kasuwar ta Igbudu ya nace kan cewa wanda ake zargin Avwerosuo Esekome ne ya sace mishi wayr amman kafin kowa ya Ankara ya gudu. Sai dai kash, a safiyar talata sai ya dawo cikin kasuwar inda aka kama shi aka hukunta shi ta hanyar saka shi yin wanka da ruwan kwata a titin na Old Welfare.

Kana kuma masu gadin suka tursasa shi da ya zaga kasuwar kuma yana amsa laifin satar wayar da yayi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG