Akwai alamar shahararren dan wasasn Liverpool Mohamed Salah, kuma wanda ya zama zakaran Afrika sau biyu zai koma da wasansa a kungiyar Jeventus a kan kudin Turai euro miliyan dari biyu.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Sky News Arabia, a shirye Juventus take ta biya euro miliyan dari biyu domin ta hada Sala da Cristiano Ronaldo su yi mata wasa.
Dan shekaru 26 da haifuwa da ya gama wasan sa a Liverpool a karon farko, ya zura kwallaye 44 a gasa da dama a Liverpool kuma akwai alamar zai zama dan wasa mafi tsada na biyu a duniya bayan Neymar da ya kafa tarihi a lokacin da ya koma da wasa Paris Saint-Germain.
Wannan babban labarin na cewa Ronaldo da shugabannin kungiyar ta kasar Italiya, sun bayyana amincewar su ga karbar dan wasan Liverpool wanda kudin sayen sa ka iya haura euro miliyan dari biyu.
Sala ya je Liverpool ne a kan kudi euro miliyan 42 a farko-farkon kakar wasa da ta gabata kuma ya zura mata kwallaye 64 a cikin wasanni 86 da ya yiwa Liverpool.
Facebook Forum