Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Najeriya Sun Lashe Gasar Kimiyya Da Fasaha Ta Duniya A Amurka


A wata gasa da aka gudanar tsakanin daliban kimiyya da Fasaha na duniya a kasar Amurka, Najeriya ce ta zo kasa ta farko da dalibanta suka lashe wannan gasar.

Kafin a nuna faifan bidiyon yadda daliban na Najeriya suka lashe wannan gasa, Jakadan Amurka a Najeriya, Mr W. Stuart Symington, ya yiwa daliban wani jawabi mai ratsa zukata.

Jakadan ya bayyana cewa, idan daliban suka yi aiki tare zasu iya mayar da Najeriya, da daukacin duniya kyakkyawan wurin zama, saboda abubuwanda zasu iya yi, ya kuma kara da cewa Amurka a shirye take domin tallafawa daliban domin cimma burinsu na rayuwa.

Jakadan ya ci gaba da jan hankalin daliban akan cewa “kimiyyar rayuwa bata tsaya kan dabaru kadai ba, amma akan mutane ne kamar ku, haka ma canza alkiblar rayuwa, ku sarrafa kwakwalwarku da rayuwarku bisa wani sinadarin da zai kawo sauyi a rayuwa.”

Cikin kasashen duniya Ashirin da Takwas da suka shiga wannan gasa, Hudu daga cikinsu ne suka zo dab da juna wato kasar Brazil da Indiya da Najeriya da kuma Amurka, kuma a cikinsu gabaki daya Najeriya ce tazo ta Daya.

Daliban sun kirkiro wata manhaja ce da jama’a zasu iya amfani da ita idan suna bukatar a yi masu ayyukan tsabatace muhalli wanda zai raba su da kamuwa da cututtuka kamar su cutar cizon sauro, da masassara dake da nasaba da tsabtar muhalli.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina Domin Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG