Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Koyon Gyaran Gashi Ta Sace Yara Biyu


Wata mata mai koyon aikin gyaran gashi mai suna Grace, tayi awon gaba da ‘ya’yan mai koya mata aiki su biyu, masu suna Faroiuk mai shekaru hudu da Kafayat mai shekaru shida.

Wannan dai ya faru ne a unguwar Okokomaiko dake Legas, kuma ya faru ne ranar Juma’a, bayan da yaran suka dawo daga makaranta. Rahotanni na nuni da cewa Grace, tace yaran su zo su rakata sayen abinci ne daga shagon gyaran gashin, daga nan sai tayi awon gaba dasu.

A cewar mahaifiyar yaran ita dai Grace, ranar Laraba ne tazo shagonta cewa tana son ta koyi aikin gyaran gashi, sai ta bukaceta ta kawo mai tsayamata sai tace a wurin kawarta take zaune sai suka ajiye cewar ranar Juma’a, zasu je ta ga gidan da take.

Suliyat Azeez, maihaifiyar yaran tace ta tafiyar wurin taron kungiyar masu gyaran gashi na unguwarsu ne cewa idan ta dawo sai suje ta ga gidan da take kafin ta dawo Grace, ta ranta ana kare da Farok da Kafayat, tun ranar juma'a har yanzu babu labari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00

XS
SM
MD
LG