Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Gubar Dalma Ta Kashe Mutane a Jihar Neja Akasarinsu Yara Ne


Yara
Yara

Jami’an kiwon lafiya a jihar Neja, sun tabbatar da mutuwan mutane ashirin da takwas a sakamakon barkewar cutar gubar dalma a karamar hukumar Rafi a jihar.

Mutane sittin da hudu ne dai suka kamu da cutar a wani wuri ginar ma’adinai a kauyen Ashara a karamar hukumar ta Rafi.

Akasarin wadanda suka mutu da kuma suka kamu da cutar yarane ‘yan kasa da shekaru biyar, haka kuma dabbobi fiye da gida dari ne suka mutu a sakamakon bullar wannan cutar.

Shugaban karamar hukumar ta Rafi Sahabudeen Isa,yace a halin da aike ciki sun dauki matakin dakatar da aikin ginar ma’adinan a yankin, tare da canja wa mutanen kauye matsuguni , kuma an tura masu dauke da cutar zuwa asibiti a jihar Zamfara domin samun kulawa ta masamman.

XS
SM
MD
LG