Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CITAD: Kaso 60 Cikin Dari Na Rikicin Kasa Na Da Nasaba Da Rashin Aikin Yi


CITAD

A shirin mu na matasa da siyasa Dandalin VOA, ya yi hira da cibiyar bunkasa fasahar sadarwar zamani, da ci gaban al’umma wato CITAD, wanda ta bayyana cewar kaso 60 cikin dari na rikicin da ake samu a kasar, na ‘yan tada kayar baya, da na Boko Haram, yana da nasaba da karancin aikin yi, musamman ga matasa.

Injiniyar cibiyar Kamal Umar ne ya bayyana haka a yayin tattaunawa da daliban jami’oi. Jami’in gudanarwa a cibiyar Injiniya Kamal, ya bayyana hakan yayin wani kaddamar da wani shiri mai suna "A Hope".

Injiniyar Kamal ya kara da cewar kasancewar kudancin kasar sun yi nisa a bangarori da dama, saboda haka zasu kara fadada shirin zuwa sauran jami’o’i.

Ya ce hanya ce ta samar wa matasa ayyukan yi. Banda haka kuma, a shirye shiryen cibiyar sun gano cewar rashin aikin yi ke haifar da yawan rikice-rikicen da ake samu, baya ga cewar matasan suna da fasaha da hikma na kirkiro wasu kayayyakin fasaha da zai ciyar da su gaba.

A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:54 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG