Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cinnaka Ya Rasu


Isma'il Baffa Ahmed CINNAKA
Isma'il Baffa Ahmed CINNAKA

Allah Yayi ma dan wasan barkwanci na Hausa, Isma'il Baffa Ahmed, wanda aka fi sani da sunansa na wasa Cinnaka, rasuwa yau talata a garin Wudil.

Cinnaka ya rasu yana da shekaru kimanin 44 da haihuwa a duniya, kuma ya bar mata guda da 'ya'ya 6.

Wani aminin marigayin, Danlami Adamu Mohammed, wanda aka fi sani da sunan Yanke-Yanke, ya fadawa DandalinVOA cewa yau da safe ne marigayi Cinnaka ya fara kukar ciwon kirji, sai aka garzaya da shi asibiti a nan garin Wudil. An rubuta masa magani, amma kafin a kawo maganin sai ya ce ag garinku.

Malam Yanke-Yanke yace marigayi Cinnaka, yayi hira da jama'a, kuma an yi sahur da shi a safiyar yau ba tare da ya koka ba, kuma dawowarsa ma ke nan daga wata tafiya.

Marigayi Cinnaka na daya daga cikin 'ya'yan kungiyar masu wasan barkwanci na Hausa dake zaune a garin Wudil na Jihar Kano wadanda kuma suka yi fice, kamar irinsu marigayi Rabilu Musa Dan Ibro da Mallam Dare.

Ga cikakkiyar hirar DandalinVOA da Malam Danlami Yanke-Yanke:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG