Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cancanta Ya Kamata A Duba Wajen Zaben ‘Yan takara - Mawaki Huzaifa


Yayin da ake gab da fara zabe a Najeriya, mawaka da dama sun mayar da hankali wajen wake gwanayensu da suka fito daga jam’iyyu daban daban, tare da tallata hajarsu domin al’umma su zabe su.

Sai dai yayin da wasu mawakan suka karkata wajen irin wannan salo na wasa ‘yan siyasa, wani mawaki ya ce yana amfani ne da basirarsa wajen fadakar da mutane domin kada su yi zaben tumun dare.

Huzaifa Sani Hassan, ya fadawa wakiliyar DandalinVOA, Baraka Bashir cewa, ya kamata jama’a su bude idanunsu domin zaben cancanta ba son zuciya ba.

Ya kara da cewa, muddin akwai dan takarar da zai kawo ci gaba ko da ba a jami’yyar da mutum yake so ba ne, a zabe shi matukar yana da kyakkyawan kudiri.

Huzaifa wanda ya fi kwarewa a fannin salon wakokin hip-hop, ya ce ya dauki wannan hanyar salon waka ce sakamakon sha’awa kamar yadda mafi yawan mawaka ke yi.

Bayan kowannen su ya sami gurbin karatu sai ya canza sheka, inda tun da farko Huzaifa wakar "Nanaye" (wakokin soyayya) shi ne fannin da ya fi maida hankali a kai.

Huzaifa ya ce wakokinsa sukan tabo batutuwa da suka shafi zamantakewa, musamman abubuwan da suka shafi rayuwar matasa ta ci ma zaune, tare da fahimtar da su muhimmancin dogaro da kai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:31 0:00

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG