Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bollywood Zata Fito Da Wanni Sabon Fim Mai Tattare Da Soyayya


Bollywood zata fito da wani sabon fim mai suna Kaabil, shi dai wannan fim mai tattare da soyayya anashuwa wanda Sanjay Gupta, ya gabatar Vijay Kumar Mishra, ya rubuta a karkashin suna (Filmkraft Production).

Wannan fim din labari ne na wasu mutane biyu mace da namiji wanda yake dukkansu makafi ne amma daga bisani suka bige da soyayya.

Shi dai wannan fim mai suna Kaabil, za’a sako shine a ranar 25, ga watan Janairu na shekara nan mai zuwa a duk fadin duniya.

Sanjay Gupta, ya bayana cewa Yami Gautam, da Ronit Roy, zasu kasance gaba gaba a fim din.

Shi wannan fim din Rakesh Roshan, ne ya shirya, shi kuwa Salim Sulaiman ya kasance mai bada sauti a ciki, an dai tara kwararru wadanda suka yi fice a fannoni daban daban na harkar fina finai, an shirya wannan fim din.

Shi dai wanna fim din a fara daukar hotonsa ne a watan Maris na wannan shekarar da muke ciki a birnin Mumbai.

XS
SM
MD
LG