Kusan shekaru ashirin birnin Vancouver, mai fama da harkokin miyagun kwayoyi a Canada, da yake kara huskantar yaduwar kwayoyin, yanzu ya rungumi wani shirin yaki da miyagun kwayoyin da a baya aka yi watsi da shi amma kuma ya yi nasara a kan masu suka, shirin da mashayan kwayoyin zasu rika zuwa suna allura karkashin kulawar likitoci.
Kamar yanda dokokin yaki da miyagun kwayoyin na Canada ta yi tanadi, an kafa wurin jinyar ne a gabashin birnin, inda harkokin miyagun kwayoyi da ‘yan bata gari ya suka mamaye. Babau hayaniya a cikin ginin kana yana da girma, akwai dakin allur inda aka shirya kananan dakunan da mashayan dan kan su zasu rika allura da magunguna da aka basu da kuma allarai masu tsafta.
A gefe guda kuma ma’aikatan nes suna sa ido, saboda idan wani zai dau maganin fiya da kima, akwai rukunin likitotci da zasu fitar da adadin da yah aura a cikin jikinsa kana bashi adadin da yake bukata. A cikin tarihi da cibiyar jinyar ta kafa tsakanin shekaru 16, babu wani mai jinya da ta mutu saboda daukar maganai fiya da kima.
A halin yanzu wasu yankunan Amurka kamar Philadelphia suna fama da yaduwar kwayar opioid, birnin da huskanci mutuwar sama da mutane dubu da dari daya a bara sakamakon shan kawayar fiya da kima, kuma wuri ne da ake hada-hadar kwayar heroin a Amurka, yanzu yankin na son ya yi amfani da salon da Canada take jinyar da shi.
Magajin garin da babban lauyan gundumar sun tabbatar da shirin na Canada. Tsohon gwamnan Pennsylvania ya kafa wata kungiya mai zaman kanta da zata tafiyar da cibiyar da ake kira Safehouse. Kana zata rika bibiyar inda mashayar suke tare da sa ido a unguwar Kensington wata unguwa mai fama da talauci, inda aka samu mutuwar masu sha opioid a cikin wannan lokaci.
Sai dai wannan shirin na huskantar cijewa daga lauyoyin gwamnati, wanda suka ce kafa cibiyar ta sabawa dokokin yaki da miyagun kwayoyi. A kokarin ba a bude wannan cibiya ba, babban lauyan Amurka a gundumar gabashin Pennsylvania, William McSwain a makon da ya gabata ya bukaci alkalin tarayya ya yi amfani da dokar shekarar 1986 ya ayyana cibiyar a matsayin wacce ta sabawa doka.
McSwin ya fadawa manema labarai cewa jinya da kwayoyi irin su heroin da fentanyl ba sune mafita ga yaki da yaduwar shan miyagun kwayoyi.
Facebook Forum