Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike: Yawan Amfani Da Shafukan Sada Zumunta Na Kawo Bacin Rai


Wayar salula
Wayar salula

Shakka babu, shafukan sada zumunta na inganta zumunci da kuma yada muhimman bayanai - kai har ma da munanan bayanai. Wannan ya sa kwararru sun yi bincike inda su ka gano cewa, hasali ma, yawan bacin ran da mutane ke fama da shi yanzu na da alaka da yawan amfani da shafukan sada zumuncin.

Wani binciken da Jami’ar Pennsylvania ta nan kasar Amurka ta fitar, ya tabbatar da cewar yawaita amfani da shafukan yanar gizo na haddasa nau'ukan bacin rai da kuncin rayuwa da dai sauransu.

Burin kafofin sada zumuncin na yanar gizo, shi ne su saka ma masu amfani da shafukan cikin nishadi, amma a bangare daya kuma ba a duba alakar hakan da lafiyar kwakwalwar bil'adama, bincike da yawa basa la'akari da mu’amalar bangarorin biyu.

Hakan ya sa tsangayar binciken halayyan dan’adam ta Jami’ar ta Pennsylvania, karkashin jagorancin Farfesa Melissa Hunt, zurfafa bincike don gano illolin da biyun kan haifar, mu’amalar yanar gizo da lafiyar kwakwalwa.

Binciken ya maida hankali akan shafukan yanar gizo na Facebook, Snapchat da Instagram, binciken ya karbi ra’ayin mutane 143 wadanda suka bayyanar da adadin lokaci da suke kashewa akan shafukan, da kuma farincikin ko natsauwa da suke samu a karshen amfani da shafukan.

Kashin farko an basu damar amfani da shafukan nasu na yanar gizo, sai kashi daya kuma aka bar u batare da shiga shafukan ba, na minti 10 a kowace rana akan kowane shafin.

An yi gwajin na tsawon sati 3, inda aka gwada bangarorin biyu. Bangaren farko sun tabbatar da cewar amfani da shafin kan haifar musu da bacin rai a kusan kowane lokaci.

Dayan bangaren kuma sun bayyana irin walwala da annashuwar da su ke samu a yayin da suka bar amfani da shafukan, musamman damar da su ke samu don ganawa da mutane da kuma bayyana wasu abubuwa da su ke damunsu a rayuwar, wanda akan basu shawarwarin yadda za su magance matsalar.

Binciken dai ya karfafa amfani da shafukan yanar gizo na haifar da bacin rai kunci, da shiga cikin wasu yanayi da ka iya kai mutun ga aikin da na sani. Bincekin ya jaddada cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin kuncin rayuwa da amfani da shafukan yanar gizo.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG