Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Basirar Rera Waka Tafi Zuwa a Cikin Nishadi In Ji Autar Waka


Jamila Ado Autar Waka
Jamila Ado Autar Waka

A shirinmu na nishadi a yau mun samu zantawa da wata kallabi tsakanin rawunna wato mace mai kamar maza Jamila Ado Mai Wuka wacce akafi sani da autar mawaka

Autar mawaka dai ta shafe shekaru tara tana harkar waka , ko da ya ke ta ce ta soma waka ne tun tana yar karama a makarantar Islamiyya ta kan yi wakar maulud baya ga kallon fina-finan Indiya wanda ya na daga abubuwan da ya sa ta tsincin kan ta a harkar waka

Jamila Mai Wuka dai ta ce ta na wakar Siyasa, hada na biki , kuma tana samun basirar rera waka ne a lokutan da ta ke cikin nishadi

Kamar kullum kuma ga al’adar wannan shiri filin nishadin DandalinVOA ya yi wa Jamila Mai Wuka tistiyen baiti daya ga dandali

A fannin tsegumi kuwa shuguban hukumar tace fina-finan Hausa ta jihar Kano sama’il Afakallahu ya ce fina-finan Indiya da ake fassara su zuwa harshen Hausa ba ya bisa ka’ida a cewarsa tamkar satar fasaha ce.

XS
SM
MD
LG