Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Ta Ware Fam Miliyan 22 Domin Sayen Dan Wasan Kungiyar Evergrande


Real Madrid ta fara tattaunawar sirri da dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta PSG mai suna Marco Verratti, dan shekaru 24 domin yiwuwar dawo warsa kulob din.

Barcelona, ta ware fam miliyan £22 don ganin ta sayo dan wasan tsakiya na kungiyar Evergrande, mai suna Paulinho mai shekaru 28 da haihuwa, Manchester United, ta na dab da sayen Romelu Lukaku daga Everton.

Chelsea, ta fada sahun zawarcin dan wasan Swansea Fernando, Llorente bayan da ta gaza wajan dawo da tsohon dan wasanta Romelu Lukaku daga Everton.

Arsenal ta nuna sha'arwarta ta ganin ta sayo dan wasan tsakiya na Frankfurt Aymen Barkok.

Leicester City, ta saka fam miliyan £20 don sayen dan wasan gaban Super Eagles, na Najeriya mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Kelechi Iheanacho.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG