Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barcelona Na Son Maye Gurbin Luis Suarez Da Aubameyang


Dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, a shekarar 2018
Dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, a shekarar 2018

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, na kokarin cike gurbin dan wasanta Luiz Suarez.

Suarez na shirin tafiya jinyar tsawon wata hudu.

A dalilin hakan, rahotanni ke nuni da cewa, kungiyar wacce ke matsayi na daya a teburin gasar La Liga ta kasar Spain da maki 43, ta fara zawarcin Pierre-Emerick Aubameyang na Arsenal.

Kungiyar ta Barcelona na neman Aubameyang ne a matsayin a aro.

Sai dai bayanai sun yi nuni da cewa, Arsenal wacce ke matsayi na 10 a teburin gasar Premier Leage na Ingila da maki 30, ta fusata da yunkurin da Barcelonan ke yi na dauke mata dan wasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga mujallar Goal.

A karshen kakar wasa mai zuwa, kwantiragin Aubameyang zai kare, amma ga dukkan alamu Arsenal na kokarin ci gaba da rike dan wasan.

A ‘yan kwanakin nan, Aubameyang ya kore raderadin da ake yi cewa zai bar Arsenal.

“Mutane sun cika kirkiro labarai na bogi, ni ina kaunar Arsenal.” Aubameyang ya ce.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG