Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baraka na Neman Kunno kai a Jami'yyar APC


Kasa da mako daya da rantsar da sabuwar Gwamnatin APC, a Najeriya, a yanzu haka wata baraka na neman kunno kai a tsakanin ‘yayan jamiyyar ta APC, kamai da rabon mikamai a jihar Neja.

Wasu daga cikin ‘yayan jamiyyar a jihar, suna korafi ne game da sabon sakataren Gwamnatin jihar Neja, da Gwamna Abubakar Sani Bello, ya nada.

Sabon sakataren Gwamnatin jihar Nejan dai Alhaji Shehu Danyaya, ya kasance ne daga karamar hukumar da Gwamna ya fito, al’amarin da wasu ‘yayan jamiyyar ta APC, suka ce bai dace ba.

Amma shuwagabanin jamiyyar ta APC, a jihar Neja, sun ce Gwamnan yayi daidai kuma hakkan bai sabawa doka ba.

Mai Magana da yawun masu korafin Garba A Bosso, yace suna zaton cewa za’a yi masu adalci, amma sai ga wannan rashin adalci ya faru.

Kakakin APC, a jihar Neja Jonathan Vatsa, yace suna baiwa jama’a hakuri kuma a shirye suke su gyara kuskure idan har ya tabbata.

XS
SM
MD
LG