WASHINGTON DC, —
Tsohon dan wasan Liverpool da Manchester City, Mario Balotelli na shirin komawa kungiyar Marseille, kamar yadda jaridun kasar Italiya suka ruwaito.
Dan shekaru 28, Balotelli wanda dan aslain kasar Italiya ne, zai koma kungiyar ta Marseille ne daga Nice a gasar Faransa ta Ligue 1 a lokacin bazara da ke tafe, inda zai saka hannu a kwantiragin Pam miliyan 1.8 har zuwa karshen kakar wasa.
Shi dai Baletolli ya yi fama da farin kwallaye a wannan kakar wasa, inda ya gaza zira kwallo ko guda a wasanni 10 da ya buga.
Ko da yake, tauraruwarsa ta haska a kakannin wasa biyu da suka gabata gasar Ligue 1 din ta Faransa, inda ya zira kwallaye 42 cikin wasannin 64 da ya bugawa kungiyar ta Nice wacce rahotanni ke cewa zai bari.
Facebook Forum