Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Balarabe Sheku Loko: A Fara Amfani Da Harshen Hausa A Kotun Sauraron Karar Zabe


Kwamared Balarabe Shehu Loko
Kwamared Balarabe Shehu Loko

Kwamared Balabarabe Shehu a hirara su da wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir, yace ya kamata kotun da ke sauraron kararrakin zabe ta dinga gabatar da bayanan kotu a harshen Hausa, domin a kasar Hausa ce, sannan mai kara da wanda ake kara dukaninsu Hausawa ne..

Kwamared Shehu ya kara bayyana cewa kotu tana bada damar amfani da yare mafi rinjaye a kotu, wanda haka zai iya bada damar amfani da harshen Hausa.

Balarabe Shehu Loko shugaban kungiyar Leaders of Tomorrow, ta jihar Kano kuma jami'in kungiyar kare hakkin bil'adama na Human Right Network ta karamar hukumar Gwale, ya ce suna barka ga yadda matasan jihar Kano suka yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a hukunci kotun daukaka kara zaben gwamnan Kano da aka yi a jiya.

Ya ce yadda matasa suka nuna halin girma, da yarda, da kaddara abu ne mai kyau, hakan ya nuna cigaba da rashin bada dama wajen amfan da su a bangaren siyasa, ko wajen cimma bukatun siyasa.

Kwamared Loko, ya kara da cewa da dama wadanda suka hallarci kotun jiya, da saurara a kafafa yada labarai ba sa iya fadan anihin abinda ya faru a kotu sakamakon basu fahimci abinda ake fada ba.

A saurari rahoto daga wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:44 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG