A yayinda ta yiwu Alaska ce jiha mafi girma a Amurka, ita ce kuma jiha mai mafi kankatar yawan al’umma. Kashi 4 cikin 5 na yankin jihar sai da jirgin sama kadai za a iya zuwa. Al’ummar Diomede na kan tsibirin Little Diomede dake tsakanin jihar Alaska da Rasha.
Ana iya hango Rusha daga tsibirin na Diomede dake jihar Alaska.
Yankin Amurka ne, amma duk da haka tazarar kilomita 4 ne suka raba babban tsibirin na Diomede dake Rusha da ake kuma kira Ratmanov.
Wani tsohon matukin jirgin saman sojan ruwa, Mike Kutyba ya sha zuwa tsibirin na Diomede sau biyu a sati a lokacin hunturu tsawon shekaru 8, idan dama ta samu ko yanayi na a kyau.
A tsibirin Diomede kauyen Inupiat, ko Inaliq yake. A shekarar 2018, kusan mutane 80 ke zama tsibirin mai fadin kilomita 7 murabba’i.
Da wuya a a ga tsiro a tsibirin saboda yanayin duwatsun dake cikinsa. Su kuma al’ummar dake makwabciyar kasar Rasha da a Da ke zama babban Tsibirin Diomede, an kwashesu an maida su hayin tsibirin, inda suka baro kuma aka maida shi sansanin sojoji.
Rayuwa bata canza ba sosai a tsibirin Little Diomede daruruwan shekaru da suka wuce. Babu hanyoyi, babu motoci, hanyoyin wucewar ruwa na karkashin kasa.
Facebook Forum