Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Sayar Da Alex Iwobi Ba - Arsenal


dan wasan Arsenal, Alex Iwobi, wanda dan asalin Najeriya ne

Arsenal ta ki amincewa da sayar da dan wasanta Alex Iwobi ga kungiyar kwallon kafa ta Everton a gasar Premier League a Ingila, wacce ta taya shi kan kudi Pam miliyan 30.

Jaridar yanar gizo ta TalkSport ce ta bayyana hakan a yau Laraba, yayin da ake shirin rufe kasuwar ‘yan wasa a gobe Alhamis.

Gidan talbijin din wasanni na Sky Sport, shi ma ya ruwaito cewa, Gunners, ta yi watsi da tayin na Everton.

A daya bangaren kuma, kungiyar ta Arsenal, tana zawarcin dan wasan Barcelona Samuel Umtiti wanda suke so su karbo shi a matsayin aro.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, kocin kungiyar Unai Emery, na kokarin ya ga ya karfafa tsaron bayansa, lamarin da ya sa yake neman dan wasan wanda dan asalin kasar Faransa.

  • 16x9 Image

    Mahmud Lalo

    Dan jarida ne da ke aiki a Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a birnin Washington, DC na Amurka. Yana da kwarewa a rassa daban-daban na kafafen yada labarai, kamar wajen hada rahoto a takadar/mujallar jarida, fannin talbijin, rediyo, yanar gizo da kafafen sada zumunta na zamani, inda ya fi mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi shugabanci na gari, ayyukan dogaro da kai, kiwon lafiya da kuma muhalli.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG