Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Yara Kadai Ke Bara Ba A Cewar Kwamared Aliyu Samba


Kwamared Aliyu Samba

Matashi kwamared Aliyu Samba, shugaban kungiyar "Mu Kawar Da Bara Movement", da ta Almajiri Child Initiatives ya ce wani gangami fadakarwa da suka gudanar a jihar Kaduna ya ja hankalin gwamnonin jihohin Arewa wajen waiwayar matsalar bara.

Kwamared Samba, dan gwagwarmaya kuma jakaddan zaman lafiya, ya ce tuni gwamnatin jihar Kaduna ta fara yunkurin fito da hanyoyin magance matsalar bara, inda ta fara lalubo hanyar sanya kananan yara, har zuwa shekara 16 da ke yawo kan tituna, shiga makarantu.

Ya ce sun fuskanci rashin fahimta daga bangaren al'’umma, inda mutane suke alakanta hakan da yara da ake turo su almajiranci, wanda ba haka abin yake ba domin ita bara ta kasu gida uku.

Ya kara da cewa akwai bara da masu nakasa keyi, ko talakawa wadanda suke cikin matsi ko kuma dattawa, da zarar an fara batun bara sai a manta da wadannan.

Kwamared Aliyu ya ce ko su wadannan da suke barar, matsala ta tsananin rayuwa ke jefa su cikin wannan yanayin. Kuma suna bukatar tallafin gwamnatin tarayya ta hanyar inganta rayuwar su.

Aliyu ya kuma ce, watannin biyu da suka wuce a wani taron gwamnonin Arewa da aka gudanar a jihar Kaduna,sun yi wani gangami, maimakon tattauna matsalar tsaro sai suka maida hankali wajen tattauna matsala ta almajirci.

Ga cikakken rahoton daga wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG