Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba a Saka Asalin Hausawa a Tallace-Tallace - Alo Bobo


Dan waka Alo Bobo
Dan waka Alo Bobo

A yau, Dandali ya samu bakunci mawaki Anas Muhammad Bello Alo Bobo mawakin Hausa hip-hop wanda ya ce ya zabi hip-hop ne domin kawo sauyin da zamani yake dauke da shi.

Ya ce amma a maimakon yadda sauran duniya ke daukar hip-hop da waka mai dauke da zagi ko rashin da’a shi ba salon da ya dauka ba kenan.

A cewar shi, maimakon haka, sai yake sanya karin magana ko azancin zance wanda a hannu guda yana koyar da darasi baya ga koyar da lugga ta Hausa.

Da haka ne yake jan hankalin matasa da ma sauran al'umma wajen gane cewar ko da akwai sauyin zamani, mawakan Hausa ma suna tafiya da zamani amma su ta hanyar ilimantarwa da kuma nashidantarwa a hannu guda.

Ya ce yana jan hankulan matasa kan muhimmanci ilimi da illar rashin mai da hankali wajen neman ilimi da illar bin abokan da ba su dace ba.

Daga cikin wakokinsa, ya ce yana wakar da ta shafi hadin kan al’umma da kauracewa rikice-rikicen da ke haifar da rarrabuwar kawun a tsakanin 'yan Arewacin Najeriya.

Daga cikin abin da ya fi ci masa tuwo a kwarya, a cewar Alo Bobo, shi ne rashin b asu dama musammam a tallace tallace da sauran abubuwan karuwa inda ya nuna korafi kan yadda ake dakko mai jin harshen Hausa ko da kuwa yana kuskure a harshen nasa da sakon da yake isarwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG