WASHINGTON D.C —
Malam Aminu Sabo Dambazau malami ne a fannin halaiya da zamantakewar dan'adam a jami'ar bayero dake birnin Kano kuma yayi mana kyakkyawan bayani akan yadda lamarin ya ke.
Koda shike jama'a da dama na cikin yanayin kuma sun san yadda auren zumunci yake, al'uma musamman ta bahaushe ta dade da samun kanta cikin wannan hali mai kara dankon zumunci da hada kan al'uma.
Malamin ya bayyana yadda zamantakewa da sauran nasarorin al'uma suka samo asali da nasaba da dangantaka tsakanin al'umomi daban daban ta hanyar auren zumunci.
Saurari cikakken shirin a dandalinvoa.com