Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aure Baya Hana Neman Ilimi - Dr Maryam Sani Ado


Dr. Maryam Sani Ado
Dr. Maryam Sani Ado

Kamar yadda muka saba kawo maku shirin mata a kowane karshen mako, Yau Dandalinvoa ya samu bakuncin Dr Maryam Sani Ado, likita ce a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Inda ta kware a fannin gwaje-gwajen cutuka wanda a turance ake kiran sa (Radiologist).

Tace ta karanta fannin likita a jami’ar Bayero Univeristy kano sakamakon sha’awar karanta fannin aikin lafiya da take da shi a zuciyar ta saboda ta tashi taga Mahaifin ta likita ne tun tana karama.

Ta kuma yi kira ga matasa cewa idan zasu yi karatu suyi kokari su karanta abunda suke sha’awa domin yin hakan ne zai saukaka masu karantu, tace tun da ta fara karatun likita bata taba samun wani kalubake ba saboda ra’ayin ta Kenan tun tana karama.

Daga karshe Dr Maryam ta kara da cewa bata yi aure ba sai da ta kammala karatunta sannan kuma tayi kira ga yan’uwan ta mata da su tashi tsaye su nemi ilimi domin kuwa aure baya hana karatu, koda aure zasu iya cimma burin su na karatun jami’a.

Aure Baya Hana Neman Ilimi - Dr. Maryam Sani Ado
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:57 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG