Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Antoine Griezmann Na Shirin Raba Hanya Da Kungiyar Atletico Madrid


Dan wasa Antoine Griezmann

Dan wasan Antoine Griezmann ya ce lokaci yayi da zai raba hanya da kungiyar sa bayan shekaru biyar.

Dan wasan gaba dan kasar Faransa mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, mai suna Antoine Griezmann ya bayyana cewar yanzu lokaci yayi da zai raba hanya da kungiyar a karshen wannan watan, bayan shafe shekaru biyar da yayi yana murza tamola da kulob din dake kasar Spain.

Griezmann, ya taimaka wa kasar sa ta lashe kofin duniya na shekarar 2019, da ya gudana a Rasha, ya kulla sabuwar yarjejeniyar kwantiraki da kungiyarsa ta Atletico Madrid har na shekaru biyar, amma a yanzu ya yanke shawarar barin kungiyar da zaran ya buga mata wasan da za ta yi da Levante, ban garen gasar Laliga na bana mako na 38 ranar Asabar mai zuwa.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tace za ta biya zunzurutun kudi har Euro miliyan 120 domin daukan dan wasan.

Sai dai a baya Barcelona tayi yunkurin sayen dan wasan Griezmann, inda shi da kansa ya yi watsi da tayin da Barcelona ta yi masa a wancan lokacin.

A shekarar da ta gabata itama kungiyar Atletico Madrid ta taba kai karar Barcelona kan cewar tana zawarcin dan wasan ba bisa ka'ida ba.

Dan wasan ya zurara kwallaye 133, a wasanni 256, da ya fafata wa Atletico Madrid, tun bayan da ya koma kungiyar daga tsohowar kulob dinsa Real Sociedad a shekarar 2014, ya kuma samu nasarar lashe kofin Europa Cup da Spanish Super Cup da kuma UEFA Super Cup, duk a tare da tawagar kungiyar ta Atletico Madrid.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG