Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin DPO Na 'Yan Sanda Da Kisan Wasu Matasa


sufeton janar na 'yan sandan Najeriya
sufeton janar na 'yan sandan Najeriya

Ana zargin DPO na ‘yan sanda ASP M. H Dass na Kiri a karamar hukumar Shelleng dake jiahr Adamawa da yiwa wasu matasa makiyaya hudu kisan mummuke.

Wannan na kunshe a wata takardar koke da ‘yan uwan mamatan suka gabatarwa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa Mal. Musa Kimo dauke da hotunan matasan lokacin da suke raye a caji ofis na Kiri da kuma na gawauwakinsu da aka yiwa daurin goro kwance a tafkin madatsar ruwa na Kiri.

Mahaifan wadanda aka kashe Mal. Kunuri Hampeto da Alh. Bakari Kem sun shaidawa muryar Amurka cewa bayaga gallazawa da barazana ga rayuwarsu lokacin da suka nemi DPO ya yi masu bayanin inda ‘ya’yansu suke, ya tilassasu biyan taran kudi sama da Naira dubu dari shida da kuma shanu.

Mori Ori daya daga cikin wadanda suka sallake rijiya da baya da yanzu ke zaman gudun hijira na sama da watanni shida ya yi bayanin yadda ya kubuta ‘yan sa’o’i kamin ‘yan bangan Talum da DPO ya mika a hannunsu su kashe shi.

Lauya mai bi wa makiyayan hakkinsu Barr, Abubakar Kolone ya ce suna tuhumar harbe Ardo Kiri babban shaida da suke dashi a tuhumar da suke yi wa DPO da wani dan bindiga da ba a san ko wanene ba mako daya bayan kashe samaran nan hudu yana kama da wani yunkuri na yin ruf-rufa game da korafinsu.

Wakilinmu Sanusi Adamu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Othman Abubakar wanda ya tabbatar da afkuwar al’amarin ya ce rundunar ta sauyawa jami’inta da ake zargi wurin aiki zuwa hedkwatanta domin tabbatar da adalci wurin kaddamar da bincike mai zurfi kan korafin da makiyayan suka gabatar.

Kisan matasan hudu na zuwa ne sakamakon tuhumar da ‘yan sanda ke yi masu na kisan tsohon kantoman yankin rayawa na Kiri Alh. Gambo a watan Afurailun 2016.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00

XS
SM
MD
LG